✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ibrahim Mustapha na El-Kanemi ya koma Masar

dan kwallon gaba a kulob din El-Kanemi Warrior da ke Maiduguri Ibrahim Mustapha ya samu nasarar canza sheka zuwa kulob din El Entag El Harby…

dan kwallon gaba a kulob din El-Kanemi Warrior da ke Maiduguri Ibrahim Mustapha ya samu nasarar canza sheka zuwa kulob din El Entag El Harby da ke Masar. Mustapha kafin canza shekarsa zuwa Masar sai da ya samu nasarar zura kwallaye tara a gasar rukunin firimiya na Najeriya a bana.
Kulob din El Harby ya ce ya dauki Mustapha ne don ya cike gibin da wani dan Najeriya Peter Ebimobowel ya bari a kulob din&nbsp bayan ya canza sheka zuwa wani kulob din.
Kulob din El-Harby dai ya gama ne a matsayi na bakwai bayan ya hada maki 52 a gasar rukunin Masar a bara.
Kafar watsa labaran wasanni ta AfricanFootball.com ta binciko Mustapha ya taba zuwa kasar Norway don neman kulob amma bai samu sa’a ba sai yanzu da ya samu nasarar komawa Masar don cigaba da kwallo.