A Juma’ar da ta gabata ce Allah Ya yi wa Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru rasuwa a hatsarin jirgin sama.
Laftanar Janar Attahiru, wanda dan asalin Jihar Kaduna ne, ya zama Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya a ranar 26 ga Janairu, 2021.
- Saudiyya ta amince ’yan kasashen waje su je aikin Hajji a bana
- Rasuwar Janar Attahiru ta girgiza ni —Na’Allah
Sai dai watanni hudu bayan kama aiki, hatsarin jirgin sama ya ritsa da shi a Filin Jirgin Sama na Kaduna, inda karar ta cimmai tare da wasu manya da kananan hafsoshin sojin kasar.
A ranar 10 ga watan Agustan 1966 aka haifi Marigayi Ibrahim Attahiru inda ya kammala Makarantar Horar da Hafsoshin Soji ta Nigerian Defence Academy (NDA) a 1986, bayan shigarsa a waan Janairun 1984.
Ya samu kwarewa a fagen aikin soji daga Armed Forces Command Staff College da ke Jaji da kuma Kwalejin da ke Horar da Kananan Hafsoshin Soji ta Nigerian Army School of Infantry dukkansu a Jihar Kaduna.
Ya ci gaba da karatu domin karo ilimi, inda ya samu shaidar digiri na biyu a Jami’ar Salford da ke Birtaniya, bayan wata babbar Diploma da ya samo a Jami’ar Nairobi da ke Kasar Kenya.
Marigayin shi ne ya maye gurbin Janar Tukur Yusuf Buratai, a matsayin Babban Hafsa Sojan Kasa na Najeriya.
Kafin samun wannan mukami, shi ne Shugaban runduna ta 82 a rundunar sojin kasar.
Sannan ya rike mukamai da dama a lokacin rayuwarsa, ciki har da Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Arewa-maso-Gabas.