Abubuwa da dama sun faru a wannan makon mai karewa, kama daga sace dalibai akalla 120 a wata makarantar sakandare a Jihar Kaduna, zuwa ga karin girman da aka yi wa Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya.
Ga wasu daga cikin labaran da muka kawo muku a makon cikin hotuna.

Shugaban Majlaisar Wakilai ta Najeriya Femi Gbajabiamila (daga hagu) yayin da yake musafaha da takwaran aikinsa na Majalisar Wakilai ta Ghana, Alban Kingsford Sumana Bagbin, wanda ya jagoranci wata tawagar ‘yan majalisar Ghana da suka ziyarci Najeriya. An dauki hoton ne jim kadan bayan Nonorabil Bagbin ya yi jawabi ga zauren Majaisar Wakilai ta Najeriya (Hoto: Ofishin Yada Labarai na Shugaban Majalisar Wakilai)