✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hutun Sallah ne ya jawo wahalar man fetur — NNPC

Kamfanin ya ce yana da wadataccen man da zai iya yin kwana 43

Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya alakanta wahalar man fetur din da ta sake kunno kai a wasu sassan Najeriya da karancin dakon shi saboda hutun Sallah.

Gidajen mai da dama dai a Abuja da Kano da Legas sun kasance a rufe.

A cewar Shugaban Sashen Yada Labarai na kamfanin, Garbadeen Muhammad cikin wata sanarwa, NNPC ya ce, “Kamfanin NNPC ya lura da sake dawowar dogayen layukan mai a wasu sassa na Abuja.

“Hakan ba abin mamaki ba ne in aka yi la’akari da karancin dakon man sakamakon dogon hutun da ake tafiya, kamar hutun Sallah Karama a wannan karon.

“Wani abin kuma da ya dada ta’azzara matsalar shi ne karin bukatar man, wacce ke faruwa a duk lokacin da mazauna Abuja suke dawowa daga hutu,” inji sanarwar.

Sai dai NNPC ya ce ya dauki matakan ganin cewa ya yi aiki da hukumomin da ke kula da rarraba shi don ganin ya wadata a ko ina.

“Muna ba dukkan mazauna Abuja da ma dukkan ’yan Najeriya tabbacin cewa muna da wadataccen mai a ajiye, wanda yawan shi ya haura lita biliyan biyu da rabi, kuma zai iya yin kwana 43,” inji kamfanin.

Rahotanni sun nuna cewa wahalar man, musamman a Abuja ranar Litinin ta sa masu amfani da motoci sun yi cirko-cirko, yayin da wasu da dama suka makara a kokarin zuwa wuraren ayyukansu.