Babban Sufeton ’yan Sanda Najeriya, Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan Mataimakin Kwamishinan ’yan Sanda, Abba Kyari bisa zargin karbar cin hanci da rashawa.
Kyari dai ana zargin sa da karbar cin hanci daga hannun shahararren matashin dan Najeriyar nan da ke fuskantar tuhuma a Amurka kan ayyukan zamba na duniya, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.
Ana zargin Hushpuppi ne da zambatar manyan kafanoni da kungiyoyin kwallon kafa da kuma daidaikun mutane a kasashensu na fadin duniya.
Wasu bayanai da matashin ya fada wa masu bincike na cewa ya taba bai wa jami’in dan sanda Abba Kyari wasu kudade domin a daure wani abokin huldarsa, zargin da Kyari ya musanta
Hukumar bincike manyan laifuka ta Amurka wato FBI, ta bukaci hukumomin Najeriya da su binciki Abba Kyari bisa zargin karbar wasu kudade a matsayin cin hanci daga hannun Hushpuppi domin ya garkame masa wasu daga cikin abokanan huldarsa.
A cikin sanarawar da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Najeriya Frank Mba ya fitar, ya ce Babban Sufeton ’yan sandan kasar ya ba da umarni domin a gano gaskiyar lamarin.
Sanarwar ta ce, “Kamar yadda aka samu bayanan zargi da kuma tuhuma daga hukumar FBI a kan daya daga cikin jami’an ’yan sandan kasar nan, Babban Sufeton ’Yan Sandan ya ba da umarnin a fara duba lamarin tukuna a nan cikin gida Najeriya.
“Hukumar ’yan sanda tana mai jaddada tsayuwarta a kan tabbatar da abin da yake na gaskiya da kuma kara karfafa alaka da Hukumar FBI da ma duk wata hukuma ta duniya.
“Muna mai tabbatar da cewa duk wani karin bayani da za a samu a kan abin da ya shafi wannan lamari, za a sanar da al’umma kamar yadda ya dace”, a cewar sanarwar.