✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hushpuppi: An kafa sabon kwamitin binciken Abba Kyari

Sabon kwamitin zai binciki gaskiyar zargin da FBI ke yi wa Abba Kyari.

Hukumar Kula da sha’anin rundunar ’yan sandan Najeriya ta PSC, ta ce ta kafa sabon kwamiti domin gudanar da bincike game da zargin da ake yi wa Mataimakin Kwamishinan yan Sandan da aka dakatar, DCP Abba Kyari.

Matakin ya biyo bayan zargin sa da ake yi wa Kyari da karbar cin hanci a hannun Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi, wanda ke fuskantar shari’a a Amurka kan ayyukan damfara ta yanar gizo.

Aminiya ta ruwaito cewa, Hukumar PSC ta dakatar da Abba Kyari, wanda shi ne Shugaban tawagar Tattara Bayanan Sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT) bisa zargin karbar cin hanci.

Sabon kwamitin na PSC zai yi aiki karkashin jagorancin Tijjani Mohammed, Darakta daga Sashen Ladabtar da ’yan sanda wanda Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Abubakar Ismaila ya kaddamar.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani ya fitar, ana sa ran sabon kwamitin zai binciki gaskiyar zargin da FBI ke yi a kan Kyari.

Kazalika, hukumar ta umarci Sufeton ’yan sanda, Usman Baba da ya gabatar mata da bayanai kan lamarin don daukar matakin da ya dace.

Dakatarwar da aka yi wa Abba Kyari ta fara aiki daga ranar Asabar 31 ga watan Yuli, 2021, har zuwa kammala binciken da ake yi bisa tuhumar da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta FBI a Amurka ke yi masa.