✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukuncin FIFA: Najeriya ta tsallake rijiya da baya

Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya ta ce Najeriya ta tsallake rijiya da baya a kokarin dakatar da ita da ta yi niyyar yi tun…

Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya ta ce Najeriya ta tsallake rijiya da baya a kokarin dakatar da ita da ta yi niyyar yi tun bayan wa’adin yin haka ya kare a ranar Litinin da ta wuce.
Hukumar ta ce ganin yadda Hukumar NFF ta koma da shugabannin hukumar na asali da ke karkashin jagorancin Alhaji Aminu Maigari ta sa yanzu ta bar Najeriya ta fafata a kowace irin gasa da hukumar take shiryawa.
Wannan dai shi ne karo na biyu da Najeriya take tsallake rijiya da baya a kokarin hukumar  FIFA na neman dakatar da ita saboda saba mata a kan wadansu sharudodi da take gindayawa kasar.
Idan za a tuna tun bayan da wani bangare a Hukumar NFF ya gabatar da zaben sabon shugaba da ke karkashin Mista Chris Giwa, Hukumar FIFA ta ce ba ta amince dsa zaben ba al’amarin da ya sa aka rika kai ruwa rana a tsakanin bangaren Alhaji Aminu Maigari da kuma na Chris Giwa.
Tuni FIFA ta bayyana cewa ba ta amince da zaben Giwa a matsayin sabon shugaba ba don haka ta bukaci hukumar ta mayar da Alhaji Aminu Maigari a matsayin shugaba kafin a gudanar da sahihin zabe ko kuma ta fuskanci fushin hukumar.
Ya zuwa ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar ta amince da bukatar FIFA inda tuni ta mayar da tsofaffin shugabannin a kan kujerunsu da ke karkashin shugabancin Alhaji Aminu Maigari.
Da hukumar FIFA ta kakabawa Najeriya takunkumi da an hana ta cigaba da fafatawa a gasar neman zuwa gasar cin kofin Afirka da ke gudana a halin yanzu da ma duk wadansu wasanni da hukumar za ta shirya nan gaba.

…Ministan wasanni ya haramta wa Maigari da Chris Giwa shiga Hukumar NFF

Jim kadan bayan tsohon Shugaban Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya Alhaji Aminu Maigari da tawagarsa sun koma kan kujerarsu a bisa umarnin Hukumar FIFA a ranar Litinin da ta gabata sai kuma aka wayi gari a ranar Talatar da ta wuce Ministan kula da harkokin wasanni na kasa Mista Tammy Danagogo ya bayar da umarnin Alhaji Aminu Maigari da tawagarsa da kuma bangaren Chris Giwa da su fice daga hukumar har sai an sasanta rikicin da ke faruwa na shugabanci a hukumar.
Ministan ya ce ya bayar da umarnin ne don ganin an samu sasanta bangarorin biyu.
Ministan ya ce idan ya kyale wani bangare cigaba da zuwa hukumar a matsayinsa na shugaban Hukumar to hakan ba zai taba kawo zaman lafiya ga bangarorin biyu ba, don haka ya dauki wannan mataki na hana kowane bangare halartar hukumar.
Sai dai Ministan ya ce ya kadu matuka da ya samu labarin Alhaji Aminu Maigari ya shiga ofis a ranar Talatar da ta wuce don cigaba da aiki a matsayinsa na shugaba duk da umarnin da ya ba shi na kin yin haka, amma daga bisani Alhaji Magarin ya tattara nasa-ya-nasa ya bar hukumar.
Ya zuwa yanzu ba a san matakin da Hukumar FIFA za ta dauka a kan Najeriya ba duk da cewa an mayar da Aminu Maigari bisa kujerarsa amma kuma Ministan Wasanni ya hana shi cigaba da gudanar da aikinsa a cikin ofishin hukumar NFF.