Gwamnatin Jihar Kano ta ce daga yanzu kwacen waya zama daidai da fashi da makami a Jihar, kuma duk wanda aka kama hukunci iri daya za a rika yanke masa da dan fashi.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida na Jihar mai barin gado, Malam Muhammad Garba ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da safiya Asabar.
- Ku yafe min wahalar da kuka sha lokacin canjin kudi – Buhari
- Filin kwallon da jirgin kasa ke bi ana tsaka da wasa
Ya ce daukar matakin ya biyo bayan taro Majalisar Tsaro ta Jihar a zamantan na bankwana, wacce Gwamna mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta.
A cewarsa, yawan faruwar kwacen waya a jihar a ’yan kwanakin nan abin damuwa ne wanda kuma ake bukatar tsatstsauran mataki kafin a iya dakile shi.
Malam Muhammad Garba ya kuma ce majalisar ta amince a kafa wata runduna ta musamman a cikin jami’an tsaro wacce za ta rika yaki da mummunar dabi’ar ta kwacen waya.
Ya kuma ce sun tattauna muhimman batutuwa kan yadda za a rantsar da sabuwar gwamna cikin nasara, inda ya ce sun tanadi kwararan mataki da za su sa a yi taron lafiya a tashi lafiya.
“Ba za a lamunci duk wani yunkuri na lalata kayan gwamnati ko na daidaikun mutane ko na ’yan adawa ba da sunan murnar rantsuwa, kuma jami’an tsaro sun yi kyakkyawan tanadi wajen dakile yin hakan,” in ji sanarwar.
Taron, a cewar Kwamishinan ya sami halartar kusan ilahirin shugabannin hukumomin tsaro a jihar da sauran mambobin kwamitin.
Mutane dai a jihar sun jima suna korafin cewa ba a hukuncin da ya dace a kan mutanen da aka kama da aikata kwacen waya a jihar, dalilin da ya sa suke ganin matsalar a kullum na dada karuwa.
Masu kwacen dai sukan yi amfani da munana makamai inda sukan ji wa mutane raunuka kafin su kwace, wasu lokutan ma har kisan kai suna yi.
Idan hakan ta tabbata dai, matakin na nufin duk wanda aka kama da laifin kwacen waya zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara 21 a gidan gyaran hali.