✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar tara harajin Kano ta yi sabon shugaba

Gwamanan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Abdurrazak Salihi a matsayin sabon shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Kano (KIRS). Kakakin gwamnan,…

Gwamanan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Abdurrazak Salihi a matsayin sabon shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Kano (KIRS).

Kakakin gwamnan, Abba Anwar wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ya ce nadin ya fara aiki ne nan take a hukumar mai alhakin tattara wa gwamnatin jiar kudaden shiga.

“Mun gamsu da gudunmuwar da shugaban hukumar mai barin gado, Bala Muhammad ya bayar a shugabacinsa na rikon kwarya daga watan Maris zuwa yau”, inji sanarwar.

Gwamnan ya yi bukaci sabon shugaban da ya jajirce tare da yin aiki tare da sauran ma’aikatansa domin samun nasarar aikin.

Sabon shubagan hukumar dai kwararre ne a kan harkokin kudi da tattara haraji, tare da kwarewar aiki ta sama da shekaru 20 a kan tafiyar da harkokin kudi.

Kafin nadin nasa, Salihi shi ne darekta a sashen tattara bayanai a jihar ta Kano, kuma ya yi ayyuka a bangarori daban-daban na gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.