Editan Aminiya ka taimake ni in isar da sakona ga Hukumar shari’a ta Najeriya, domin tauye mini hakkina da Kamfanin OMG ya yi. Motar su ta kade ni na karye a baya da kafa a shekarar da ta gabata (2015), na kuma shafe fiye da wata 10 a kwance, har suka yi alkawarin biyan diyya, amma babu ko kobo har yanzu. Kuma lauyan da yake taimaka mini idan na yi masa waya sai kawai ya yi ta yi mini fada, ko kuma ya ki dauka. A halin yanzu Hukumar taimaka wa masu rauni da lauyoyi wato Legal Aid Council, ta ba ni takarda in kai Kalaba inda aka aikata wannan laifi. Duk da haka ni ina son yin kira ga kungiyoyin kare hakkin dan Adam da Hukumar Shari’ar ta kasa ta taimaka mini da sauran wadanda aka tauye musu hakki. Domin muna da yawa, wasu ma ba su san inda za su kai kara ba, ko kuma rashin kudin daukar lauya kamar ni ke nan. Sannan ina kira ga kafofin yada labarai da su bincika labarin yadda kamfanonin ’yan kasashen waje ke kassara rayuwar ’yan kasar nan ba tare da an biya diyya ko kudin magani ba. A karshe ma su kyale wanda suka cutar a wulakance. Akwai talakwan kasar nan da ke fama da matsalolin tauye hakki, don haka akwai bukatar hokum,ar shari’a ta Najeriya ta ware wani sashe da za a smau saukin kai mata koke; ita kuma bi kadin gaskiyar mai gaskiya a ba shi hakkin sa.
Daga AbdulMajid Rufa’i Kurna Kano. 08107139629.
Hukumar Shari’a ki kwato mini hakkina
Editan Aminiya ka taimake ni in isar da sakona ga Hukumar shari’a ta Najeriya, domin tauye mini hakkina da Kamfanin OMG ya yi. Motar su…