✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama hodar iblis a gidan wani basarake

Ma’aikatan Hukumar Hana Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), sun tono wasu curi na hodar iblis da hodar heroin da aka boye a fadar wani…

Ma’aikatan Hukumar Hana Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), sun tono wasu curi na hodar iblis da hodar heroin da aka boye a fadar wani basarake a Jihar Anambra.

Jami’an Hukumar reshen Jihar Anambra sun gano hodar iblis mai nauyin giram 58.5 da kuma hodar heroin mai nauyin giram 13.9 a gidan wani mashahurin basaraken gargajiya a jihar.

Kwamandan Hukumar na jihar, Muhammadu Misbahu Idris, ya ce dogaran fadar na taimaka musu wajen gudanar da bincike domin gano dillalin wannan kunshi na miyagun kayan maye.

Haka kuma jami’an hukumar sun cafke wani dillalin miyagun kwayoyi, Hassan Bishi Taiwo, da kunshi uku na hodar iblis da ya boye a jikin jakarsa kamar yadda Kakakin Hukumar, Femi Babafemi ya bayyana a ranar Litinin.

Da misalin karfe 1.30 na ranar Juma’ar da ta gabata ce jami’an NDLEA suka damke mutumin a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Murtala Mohammed da ke jihar Legas, bayan saukarsa daga jirgin kamfanin Ethiopian Airlines.

Shugaban Hukumar NDLEA a reshenta na filin jirgin saman Legas, Ahmadu Garba, ya ce an cafke Mista Taiwo ne yayin isowar birnin na Iko daga birnin Addis Ababa na Kasar Habasha.

Aminiya ta samu cewa, an cafke wani kamfanin safarar miyagun kwayoyi da giram 500 na hodar iblis da ake shikin fita da ita zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa wacce aka boye cikin wani kwali mai dauke da tufafi.

Kazalika, an cafke kamfanin da giram dubu na tabar wiwi da aka boye a cikin wasu kwalaben man shafawa da ake shirin fita da su zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma giram 500 na kwayoyin ketamine da ake shirin fita da su zuwa Amurka wanda aka boye a cikin kayayyakin gidan tarihi.

Mista Garba ya kara da cewa, an kuma cafke kamfanin da giram 480 na kwayoyin metamphetamine da ake shirin fita da su zuwa kasar China.

Da yake jawabi a kan lamarin, Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya-Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya, ya yaba wa kwazon jami’an hukumar dangane da wannan gagarumar nasara da suka samu.