Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa (NCC) ta mika wa kungiyar Mata Ma’abuta Kimiyyar Sadarwa ta Najeriya (NIWIT) kyautar kwamfutoci guda biyar. Wannan ya biyo bayan wani kwas da gasa da hukumar ta reshen Jihar Oyo tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Oyo suka shirya wa ’ya’yan kungiyar da ke makarantun sakandare a shiyyar Jihar Oyo.
A yayin bikin mika masu wadannan komfutoci da ya gudana a hukumar NCC, Abuja, Shugaban NCC, Farfesa Umar danbatta, wanda Daraktan Al’amuran Jama’a na hukumar, Mista Tony Ojobo ya wakilta, ya bayyana tarin alfanun harkokin sadarwa ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya. Kamar yadda ya ce: “Harkokin kasuwanci daban-daban, kamar banki, shakatawa, sufurin sama, kiwon lafiya da sauransu, suna samun bunkasa ta amfani da harkokin sadarwa na zamani.” Ya kara da cewa, kimiyyar sadarwar zamani na taimakon al’umma a harkokinsu na rayuwa, yadda a saukake, mutum na zaune a gidansa zai iya gudanar da aikinsa ko sana’arsa iri daban-daban.
Ya ce shugaban hukumar NCC ya kirkiro shirye-shirye daban-daban don taimaka wa dalibai a makarantun sakandare domin su nakalci harkokin sadarwa na zamani, ta hanyar ba su kyautar na’urori da kuma shirya masu kwasa-kwasai ta wannan fanni. “Wannan zai ba su damar su yi gogayya da kininsu na ko’ina a duniya,” inji shi.
Haka kuma shugaban ya roki daliban da su yi kokarin fadakar da ’yan uwansu dalibai mata, domin su shiga cikin harkokin kimiyyar sadarwa, kasancewar akwai karancin mata a cikin harkar. Ya kuma yi alkawarin cewa hukumar ta NCC za ta karfafa hadin gwiwa da kungiyar tasu, kamar kuma yadda ya ba da shawarar yin hadin gwiwa da Ma’aikatar Al’amuran Mata da Ma’aikatar Al’amuran Ilmi domin rainon yara mata cikin harkar ta sadarwa, musamman a makarantun gwamnati, inda dalibai mata ba su cika samun damar tu’ammali da kimiyyar sadarwa, kamar sauran kininsu na makarantu masu zaman kansu ba.
Shugabar tawagar, wacce ita ce shugabar kungiyar ta kasa, Dokta Florence Babalola, ta yaba da karimcin hukumar NCC, inda ta yi alkawarin yin amfani da kungiyar ta mata wajen bunkasa amfani da kimiyyar sadarwa a tsakanin daliban makarantu. Kamar yadda ta ce, amfanin kungiyar shi ne, domin ta kawo daidaitoni tsakanin masu amfani da kimiyya, maza da mata. Ta ce za ta yi haka ne wajen shirya wa dalibai mata kwasa-kwasai, wadanda za su koya masu hikimar tu’ammali da na’urorin sadarwa, har ya zuwa yadda za su iya zama masu kera su wata rana. Ta ce za su ci gaba da amfani da wurare daban-daban da ke akwai na kimiyyar sadarwa, mallakar NCC wajen ba yara mata bita, domin cin ma burinsu a wannan fage.