✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Kwastam ta kame bindigogi fiye da dubu a Lagos

Hukumar Shigi da Fici ta kwanstam ta sake kama bindigogi dubu daya da dari daya a tashar bakin teku ta tinka da ke jihar Legas.…

Hukumar Shigi da Fici ta kwanstam ta sake kama bindigogi dubu daya da dari daya a tashar bakin teku ta tinka da ke jihar Legas.
Hakan ya bayar da adadin bindigogi dubu biyu da dari daya da goma da hukumar ta kwace a jihar a watanni bakwai da suka gabata.
Shugaban Hukumar, Kanar Hameed Ali mai ritaya wanda ya tabbatar da lamarin ya ce an boye makaman ne a cikin wata kwantena.
Ya ce jami’an hukumar ne suka gano makaman yayin da suke binciken kwakwafa na kwantenoni da aka sauke a tashar.