✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Kwastam ta kama jarkokin fetur fiye da 500 a hannun ’yan Boko Haram

Hukumar Kwastam ta tabbatar da kame jarkokin man fetur fiye da dari biyar, sannan ta yi nasarar toshe hanyoyin da ‘yan ta’addar ke bi don…

Hukumar Kwastam ta tabbatar da kame jarkokin man fetur fiye da dari biyar, sannan ta yi nasarar toshe hanyoyin da ‘yan ta’addar ke bi don sayo wannan mai daga dajin Sambisa.

Konturolan Hukumar Kwastam mai kula da jihohin Adamawa da Taraba, Francis Adetoye ya bayyana wannan nasarar da suka samu a lokacin da ya gana da manema labarai, domin nuna musu jarkokin wanda suka kama hanyar Karamar Hukumar Madagali da Mubi na Jihar Adamawa.

“Ma’aikatar hukumarmu wadanda ke bakin aiki a hanyar Karamar Hukumar Mubi da Madagali ne suka kama wata babbar motar ‘Mitsubushi’ dauke da wadannan jarkoki fiye da dari biyar cike da man fetur,” inji shi.

“Direban motar da kuma wadanda ke cikin motar suna hango ma’aikatanmu sai suka yi sauri suka shige daji a guje. Muna kyautata tsammanin cewa wadannan jarkokin man za a kai dajin Sambisa ne,” inji shi.

Francis ya kara da cewa ma’aikatansu takwas sun sha da kyar kwanakin baya a hanyar garin Wuro Bokki da ke Jihar Adamawa.

Ya ce a yayin da hukumarsu ke kokarin kama masu laifi a hanyar wani rafi, wanda ke tsakanin kan iyakar Kamaru da Najeriya ne tsagerun suka ci karo da su a kan babur din haya a yayin neman guduwa.

Ya kara da cewa an samu raunuka a wannan lokacin, domin tsagerun sun gayyato mutanen kauyen da ke kusa da rafin domin su taya su fada da su.

Adetoye ya ce daukin da matakan tsaro da masarautar suka kawo musu ya sa suka sha da kyar a tsakanin tsagerun da mambobinsu.

“Daga watan Janairu zuwa Yuli, hukumarmu ta yi nasarar samar da kudi Naira miliyan N111.745 wa gwamnati”. Inji shi.

Francis ya bayyana cewa sun samu kudi a  kalla Naira miliyan ashirin da shida a watan Yuni, a shekarar 2017.

Ya ce duk da kalubalen da suke fuskanta na yakar tsagerun a Arewa maso Gabas a jihohin Adamawa da Taraba da sauransu, hukumarsu har ta wuce irin yawan nasarori da aka gindaya mata, in an yi la’akari da rahoto a wannan watan Yuni.

Ya yi gargadi ga masu irin wadannan harkar da su nemi aiki cin halaliyarsu, kuma su bar wadannan aiki, domin in har suka kama su za su hukunta su.