A ranar Litinin 24 ga Agustan bana ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shugabannin sabuwar Hukumar Kula Da Nakasassu ta Kasa, (NCPWD).
Kakakin Shugaban Kasa Mista Femi Adesina, yayin sanar da hakan ya ce Dokar Hana Nuna Wariya ga Nakasassu ta 2019 ce ta tanadi kafa hukumar.
Hukumar, a karkashin Ma’aikatar Agaji da Jinkai da Sadiya Umar Farouk ke jagoranta, za ta samu shugaba da mambobi shida wadanda dukkanninsu nakasassu ne daga shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida.
Wadannan mutane ne za su jagoranci Majalisar Gudanarwar Hukumar na tsawon shekara hudu kuma za a iya kara musu wa’adin shekara hudu da amincewar Majalisar Dattawa.
- ‘Bara kaskanci ne gare mu nakasassu’
- Najeriya ta yi alkawarin damawa da nakasassu
- Neman aiki: Nakasassu sun yi wa AMCON zanga-zanga
Dokar ta kuma tanadi nada Babban Sakataren Hukumar, wanda ke karkashin Hukumar Gudanarwar, don aiwatar da ayyuka da tsare- tsaren hukumar.
Shi ma wajibi ne ya kasance nakasasshe da zai yi shekara biyar sannan za a iya kara masa wa’adi na biyu.
Sanarwar Fadar Shugaban Kasar ta bayyana sunayen wadanda aka nada da kuma yankinsu karkashin jagorancin Alhaji Hussaini Suleiman Kangiwa daga Arewa maso Yamma a matsayin shugaba.
Wakilan hukumar sun hada da Mista Oparaku Onyejelam Jaja, Kudu maso Gabas; Misis Philomena Isioma Konwea, Kudu maso Kudu; da Omopariola Busuyi Oluwasola, Kudu maso Yamma.
Sauran su ne Amina Rahma Audu, Arewa maso Yamma; Misisi Esther Andrew Awu, Arewa ta Tsakiya; Abba Audu Ibrahim, Arewa maso Gabas: sai kuma Mista James Dabid Lalu, Babban Sakatare, daga Arewa ta Tsakiya.
Jim kadan da nada shugabannin hukumar sai Ministar Agaji da Jinkai, Sadiya Umar Farouk, ta bayyana cewa ta cika nata alkawarin, ko kuma burinta ya cika na ganin an kafa hukumar.
Burina ya cika —Minista Sadiya Farouk
A wata sanarwa da Hadimarta kan Sadarwa da Watsa Labarai, Hajiya Halima Oyelade ta fitar kwana uku da nada shugabannin hukumar, Ministar ta ce tunda aka nada ta a 2019 ta sha alwashin ganin an kafa Hukumar Nakasassu ta Kasa kuma ta fara aiki.
“Wannan ranar farin ciki ce gare ni saboda burina ya cika, cewa wani sashi na masu matukar bukatar tallafi da nake jin tausayinsu.
“A karshe sun samu hukumarsu har an nada mata shugabannin da za su tafiyar da al’amuranta, ta kare hakkokinsu, ta sama masu kyakkyawan yanayi da zai inganta rayuwarsu, har su ba da tasu gudunmawa ga cigaban kasa”, inji ta.
Ministar ta yaba wa Shugaba Buhari kan rattaba hannu a kan Dokar Yaki da Nuna Wariya ga Nakasassu ta 2019 a bara, wadda ta ba da damar kafa hukumar.
“Amincewa da nadin Shugaba da Babban Sakatare da mambobin Majalisar Gudanarwar Hukumar, Mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara nuna sadaukarwarsa ga batun inganta rayuwar marasa galihu a Najeriya, kuma ya ba su damar su samu hakkokinsu a matsayinsu na ’yan kasa”, inji ta.
Ta taya nakasassun Najeriya wadanda ta ce sun kai miliyan 30 murnar babbar nasara da aka samu, ta kuma nemi su yi amfani da damar don inganta rayuwarsu.
Minista Sadiya ta taya shugabannin hukumar murna, inda ta ce: “Ina taya ku murna, kuma ina kira ku dauki wannan nadi a matsayinku na shugabanni na farko na hukumar ku kafa harsashi mai karfi don hukumar ta tsaya da kafafunta wajen inganta rayuwar sama da mutum miliyan 30 da ke da nakasa a Najeriya”.
Daga nan sai ta ce, “Ayyukan hukumar sun hada da fito da tsare-tsare da manufofin da suka dace tare da aiwatar da su don ilmantar da nakasassu da kyautata rayuwarsu da tsara hanyoyin inganta rayuwarsu ta hanyar sauya tunanin mutane su daina yi musu kallon raini”.
Ta ce da zaran Majalisar Dattawa ta amince da nadin, hukumar za ta fara aiki gadan-gadan.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi wadansu daga cikin nakasassun game da kafa hukumar ta NCPWD da kuma abin da suke fata sun bayyana ra’ayoyi kamar haka:
Mafarkinmu ne ya tabbata —Injiniya Shaga
Injiniya Musa Shaga shi ne Shugaban Kungiyar Nakasassu ta Kasa, Reshen Jihar Kano; ya shaida wa Aminiya cewa kafa Hukumar Kula da Nakasassu ta Kasa mafarkinsu ne ya zama gaskiya.
Ya ce sun dauki sama da shekara 20 suna fadi-tashin ganin an samar musu da hukuma ta kashin kansu.
“Mun dade muna gwagwarmaya wajen ganin an samar mana da hukuma domin an dade muna kai kukanmu gare ta.
“Mun ji dadin abin da Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari ya yi na kafa wannan hukuma”, inji shi.
Injiniya Shaga ya kara da cewa suna sa rai wannan hukuma za ta zame musu gata ta kuma share musu hawaye kan matsalolin da suke fuskanta.
“Muna sa ran idan hukumar ta yi aiki yadda ake so, ta magance matsalolinmu kashi 70 zuwa 80.
Muna da matsaloli da yawa da suka shafi harkar iliminmu da ta ’ya’yanmu da sha’anin lafiya da fannin shari’a da sauransu.
“Misali ko a gine-ginen gwamnati ba a la’akari da yanayinmu wajen yin gini don da zarar wani abu ya kai nakasasshe wadannan wurare sai a ga yana fuskantar matsala kwarai da gaske.
Haka a daukar aiki ba kowanne ake ba mu ba don sau da dama mutum ya yi karatu yana da duk abin da ake nema wajen daukar aiki, amma sai a ki daukar sa a dauki wanda bai kai shi ba don kawai yana da lafiya, wannan ba daidai ba ne”, inji shi.
A cewarsa karin farin ciki gare su, shi ne yadda aka ce kashi 70 zuwa 80 na shugabancin hukumar zai tafi ga nakasassu ne wadanda ya ce sun san matsalolin ’yan uwansu kuma ana sa ran kwalliya za ta biya kudin sabulu.
Injiniya Shaga ya ce, “Mun sha ba gwamnati shawarwari kan abin da za ta yi don kyautata rayuwar nakasassu amma ta yi watsi da su.
“Muna da masu ilimi a cikinmu a samar musu aikin yi, wadanda suka iya sana’oin hannu a ba su jarin da suke bukata.
“Kungiyoyi masu zaman kansu na horar da mutanenmu sana’o’in hannu, amma maimakon gwamnati ta tallafa musu da jarin da za su yi sana’ar sai ta yi watsi da su.
“To ba a samu wanda ya taimake su ba, dole su yi bara su nemi abinci don su rayu”, inji shi.
Abin farin ciki ne sai dai… Sarkin Makafi
Sarkin Makafin Gundumar Tudun Wadan Kaduna, Malam Bello Abubakar Talata Mafara ya ce, kafa hukumar da Gwamnatin Tarayya ta yi abin farin ciki ne gare su, sai dai za su so a debi ma’aikata nakasassu musamman shugabanninta.
“Idan aka diba daga cikinmu in ba a yi mana ba, mun san namu ne ba su yi ba amma abin farin ciki ne tunda da ba a yi da mu, kuma Hausawa na cewa zo ka ci tuwo ya fi tuwon dadi”, inji shi.
Ya bukaci hukumar ta mayar da hankali kan mabarata wadanda aka ce ba a son su yi bara.
“Ya kamata a san adadin mu mabarata da yadda za a taimaka wa masu son yin sana’a, kuma masu sauran karfi a ba mu jari mu yi sana’a,” inji shi.
Shi kuwa Sarkin Majalisar Kutaren Jihar Kaduna, Malam Idrisu Garba cewa ya yi: “Mun ji a rediyo cewa an kafa hukumar kula da nakasassu a kasa har an saka hannu amma ba a neme mu ba ballantana mu nemi jama’armu.
“Kuma tunda aka kafa hukumar babu wanda muka gani ko ya neme mu wanda ka ga ke nan ba mu da abin cewa a yanzu mun zura ido ne mu ga me zai tafi a kan abin”.
Ya ce, su da suke shugabanni kamata ya yi a neme su don su zauna da al’ummarsu, su sanar da hukumar bukatunmu a rubuce.
“Idan muka bayyana ra’ayinmu yanzu zai zama je-ka-na-yi-ka ke nan. Amma muna fatar alheri kuma a shirye muke mu ba da shawara idan an neme mu”, inji shi.
Shugabanninta ba nakasassu gama-gari ba ne —Zannah
Kwamared Muhammadu Zannah, nakasasshe ne da ke jagorantar wata kungiyar karfafa nakasasu a Najeriya, ya shaida wa Aminiya cewa wadanda gwamnati ta ba jan ragamar hukumar ba nakasassu gama-gari ba ne, wadanda su ne kashi 99 cikin 100 na nakasassun Najeriya.
“Gwamnati ta nada wadanda suke karkashin kungiyar habakar nakasassu a matakin tarayya da jihohi.
“Wadannan mutane ba su san ciwon nakasassun kasar nan ba, ba su taba fitowa kare hakkin wani nakasasshe da aka zalunta ko aka tauye masa hakki ba, illa kawai da su ne gwamnati ke amfani idan ana so a nuna cewa ana yi da nakasassu, shi kuma nakasasshe na kan hanya ko na karkara bai san abin da ake yi ba,” inji shi.
Ya ce idan gwamnati na so matakin ya inganta rayuwar nakasassun to ta shigar da shugabannin nakasassun na zahiri da suka hada da sarakunan makafi da na guragu da na kutare wadanda ake da su a ko’ina a sassan kasar nan.
Buhari ya yi abin yabo —Shehu Dumus
Malam Shehu Isa Dayyanu Dumus, nakasasshe ne da ya ce bai taba yin bara ba a rayuwarsa, wanda a yanzu yake harkokin kasuwancinsa a filin jiragen sama na Legas.
Ya shaida wa Aminiya cewa, matakin da Shugaba Buhari ya dauka na kafa hukumar abin yabo ne, kuma abu ne da suka dade suna jira.
Ya ce da wannan tsari ne nakasasshe zai samu cin moriyar ’yancinsa a matsayinsa na dan kasa kamar kowa.
“A gaskiya mun yi matukar farin ciki da wannan hobbasa ta Shugaba Buhari, babu abin da za mu yi sai yi masa addu’a, domin wannan mataki shi ne zai ba nakasassu dama da ’yancin rayuwarsu kamar kowa”, inji shi.
Shehu Dumus ya ce yana ganin nakasassu za su ci gajiyar hukumar inda ya yi fata gwamnati ta sanya ido ta tabbatar ana yin abin da ya kamata.