A al’adar Bahaushe ba sabuwar aba ba ce game da aurar da masu lalurar nakasa iri daya a tsakanin junansu.
Wannan ya sa ake samu gurgu ya auri gurguwa, makaho ya auri makauniya, kuturu ya auri kuturwa da sauransu.
Aminiya ta yi kokarin binciko dalilan da suka sa Bahaushe ke da wannan al’ada.
Kuma a binciken nata ta gano cewa masu lalurar kuturta su ne kan gaba wajen auren masu lalura irin tasu, inda zai yi wahala ka samu wani ko wata mai dauke da wannan larura ya ko ta auri lafiyayye.
Hasali ma kebance su ake yi gefe guda ba su shiga cikin jama’a kamar sauran masu nakasa abin da wasu ke gani ana nuna masu kyama da tsangwama a cikin al’umma.
Amma guragu da kurma da makaho ba su fiye fuskantar irin wancan kyama ba, sukan zauna cikin jama’a kamar sauran lafiyayyun mutane, duk da akan samu a manyan garuruwa an ware unguwa ta musamman domin masu nakasa.
Sai dai duk da haka da haka, idan aka zo batun aure akan dan samu tangarda musamman idan mai nakasa ya ga mai lafiya yana so ko kuma mai lafiya ya ga mai nakasa yana so.
Galibi dai talakawa ne suka fi samun irin wannan tangarda inda masu abin hannu daga kowane bangare ba su fiye samun wannan matsala ba.
Aminiya ta ji ta bakin wasu nakasassu inda suka bayyana mata yadda suke kallon wannan al’ada a rayuwarsu.
Abdullahi Musa, wani gurgu da ke zaune a garin guragu da makafi na Karmajiji da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja, ya bayyana wa Aminiya cewa batun auren gurgu da mai lafiya yana yiwuwa, amma sai dai akan samu tangarda a yayin neman auren.
“Iyalina mai lafiya ce ba ta da nakasa ko kadan, amma lokacin da na gan ta ina so, na hadu da kalubale iri-iri, amma a hankali da Allah Ya kaddara cewa matata ce komai ya wuce muka yi auren soyayya ga shi yanzu ’ya’yanmu hudu tare,” in ji Abdullahi.
Sai dai kuma Usman Ayuba ya ce a iya saninsa ba a fiye samun wata matsala ba in dai har an samu soyayya a tsakanin masoyan, inda ya ce dama shi aure soyayya ce ke gina shi, kuma idan mutum yana son mutum bai duba wata nakasa da wanda yake so a matsayin abin da zai hana shi auren dayan.
“Idan ka ga an samu tangarda to dama babu soyayya ce.
“Lokacin da na tashi aure ban takaita kaina cewa dole sai na auri mai nakasa irin tawa ba, saboda ni ma larura ce Allah Ya dora min, kuma tana kan kowa, kuma ko da na samu wacce nake so ban yi wata-wata ba na bayyana soyayyata gare ta kuma ta amince min,” in ji shi.
Da Aminiya ta bayyana masa cewa yakan yi wahala a ga mai larurar kuturta ya auri lafiyayyen mutum, sai ya ce masu larurar kuturta ba su daga cikin wadanda za a sa cikin nakasassu, su marasa lafiya ne da suke fama da wata cuta wadda za su iya warkewa daga wannan cuta, kuma sukan yi gadon wannan cuta.
Ya kara da cewa bai kamata mai cikakkiyar lafiya ya auri mai larurar da zai iya dauka ba, kuma hakan bai takaita a kan kuturta ba.
Ya ce, “Zai yi wahala ka ga gurgu ya haifi gurgu, ko makaho ya haifi makaho, amma kuturu abu ne mai sauki ya haifa, saboda cuta ce mai yaduwa yake tare da ita.”
Har wa yau, Aminiya ta ji ta bakin Sarkin Guragun Abuja, Alhaji Muhammad Sulaiman Katsina, ya ce ko daya ba ya da mata gurguwa matansa lafiyayyu ne, kuma haka nan wasu hakimansa da wakilansa a sauran wurare.
Dokta Mu’azu Sa’adu, masani ne a kan Harshe da Al’adar Bahaushe a Sashin Nazarin Harsuna da ke Jami’ar Sule Lamido da ke Jihar Jigawa, ya yi fashin baki a kan hikimar da ta sa Bahaushe tun tale-tale ke hada masu nakasa iri daya auratayya.
Ya ce: “Hikimar da ke cikin hada auratayya a tsakanin masu nakasa iri daya ita ce Bahaushe ya yi imani da lamarin nan na kwarya ta bi kwarya, idan ta bi akushi za ta ji kunya.
Kuma ya yarda da cewa kowace kwarya da abokiyar burminta. Bisa dabi’a ta dan Adam, koyaushe yakan fifita kansa ne kasawa ya tura ta ga wani, don haka idan aka dauko mai wata lalura aka dora wa mai lafiya, ba za a samu natsuwa da zaman lafiya ba, idan aka samu gurgu ya je ya nemi gurguwa ko aka hada su auren to sai ka ga an zauna lafiya, ba mai yi wa kowa gori.”
Baya ga haka ya ce Bahaushe ya yi imani da gado, shi ya sa yake tsantseni wajen hada zuriya.
Ya yarda cewa akan yi gadon kuturta, maita, rowa da rashin kunya da sata da tsiya, wannan ya sa idan saurayi ya nemi aure a wani gida za ka ji iyayensa sun hana sun ce kada ka je ka kawo man dangin tsiya.