✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar kiyaye hadurra ta tallafa wa majinyata da abinci

A tsare-tsaren ayyukan wayar da kan al’umma da hukumomin  kiyaye hadurra na duniya suka gudanar, don makon kiyaye hadurra na duniya  da aka gudanar a makon…

A tsare-tsaren ayyukan wayar da kan al’umma da hukumomin  kiyaye hadurra na duniya suka gudanar, don makon kiyaye hadurra na duniya  da aka gudanar a makon da ya gabata. Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa ta shiyar Saminaka da ke Jihar Kaduna, ta tallafa wa majinyata da suke kwance a Babban Asibitin Saminaka a sanadiyar hadari da kayayyakin abinci.

Da take zanta wa da wakilinmu, Kwamandan hukumar ta shiyyar Saminaka ACC Hauwa Abdul Lurwan ta bayyana cewa sun je asibitin ne domin su gaida marasa lafiya da suka yi hadari kuma suka tallafa masu da kayayyaki abinci.

Ta ce wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka gudanar na makon kiyaye hadarurruka na duniya.

Ta ce sun zagaya dukkan masu ruwa da tsaki kan  ayyukan kiyaye hadarurruka, inda suka musu bayani kan abubuwan da suka kamata masu tuki su rika yi, a kan hanyoyi.

Ta kara da cewa sun je tashohin mota, inda suka yi gangamin wayar da kan direbobi abubuwan da suka kamata su rika yi a kan hanyoyi, kamar yin takardun mota da lasisi. Kuma sun gargadi direbobi kan su guji mugun gudu da daukan kaya da mutane fiye da ka’ida a motocinsu.

Haka kuma ta koka kan matsalolin da suke fuskanta a wannan shiya na yadda jama’a suke shigar masu aiki suke goyon bayan direbobin da suka aikata laifi a kan hanyoyin.

Ta ce sau tari idan direbobi suka yi laifi, idan suka kama su sai jama’a su taru su hana su yin aikinsu.

Ta ce ya kamata jama’a su fahimci cewa su sun zo ne domin su yi gyara, ta yadda za a magance hadurran abubuwan hawa a wannan yanki.