✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar JAMB za ta gudanar da jarrabawar gwaji ranar 23 ga Maris

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya (JAMB) ta ce za ta shirya wa daliban da suke neman shiga manyan makarantun  jarrabawar gwaji a…

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya (JAMB) ta ce za ta shirya wa daliban da suke neman shiga manyan makarantun  jarrabawar gwaji a ranar Asabar 23 ga Maris din nan.

Kakakin Hukumar JAMB, Fabian Benjamin ya ce daga shekaranjiya Laraba, duk dalibin da zai rubuta jarrabawar ta bana zai iya gurza takardarsa da za ta ba shi shaidar cancanta.

Ya cewa hukumar ta kirkiro da jarrabawar gwajin ce a shekarar 2017 domin ba dalibar dama su kara shiri don fuskantar jarrabawar ta ainihi, kuma hakan zai ba su dama su koyi yadda ake gudanar da jarrabawar ta hanyar amfani da kwamfuta, musamman daliban da ba su saba amfani da na’urar kwamfuta ba.

Ya ce “Hukumar JAMB ba ta son ta ga an bar wani dalibi a baya, wanda haka ne ya sanya ta kirkiro wannan tsari na gudanar da jarrabawar gwaji da sauran wasu matakai da za su taimaka wa daliban domin rubuta jarrabawar yadda ya kamata. Haka kuma hukumar ta shigo da wata dabara, inda dalibai za su yi amfani da hakoran kwamfuta guda tara wajen rubuta jarrabawar.”

Ya kara da cewa hukumar tana amfani da wannan tsari na jarrabawar gwaji ne da nufin tabbatar da cewa hukumar ta shirya sosai domin fuskantar jarrabawar ta ainihi sosai, kamar kuma yadda take amfani da wannan tsari domin gwada yadda daliban suka shirya wa ita kanta jarrabawar ta JAMB.