✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar INEC da raba katin zabe na dindindin

A fili yake cewa akwai matsala dangane da yadda hukumar zabe ta kasa (INEC) take raba katin zabe na dindindin. Shirin raba katin zaben yana…

A fili yake cewa akwai matsala dangane da yadda hukumar zabe ta kasa (INEC) take raba katin zabe na dindindin. Shirin raba katin zaben yana tafiyar hawainiya, kuma ga dukkan alamu ba za a kammala shi kafin wa’adin da Hukumar INEC ta diba ba. Wannan al’amarin raba katin zaben ya haifar da cece-kuce, inda jama’a da dama suka shiga zanga-zanga.
A yanzu masu zabe tuni suka kasance cikin dimuwa da fargaba tun da Hukumar INEC ta ce duk wanda bai mallaki katin zabe na dindindin ba, to ba zai jefa kuri’a a zaben 2015 ba, kodayake daga baya ta ce za a iya kada kuri’a da katin zabe na wucin gadi. A yanzu sauran watanni kadan a yi zabe mai zuwa, sannan kashi 70 cikin 100 ba su karbi katin zabe na dindindin ba.
Jihohi masu yawa sun yi korafin adadin katunan da aka kai musu ba su kai adadin wadanda suka yi rijista a jihohinsu ba, inda wadansu suka ce jihohin da jam’iyyar adawa ke mulki ne aka fi samun ire-iren wadannan matsalolin, an kuma yi hakan ne da gayya don kawai an hana jama’arsu yin zabe. INEC ta karyata batun cewa ta yi hakan ne don taimaka wa jam’iyya mai gwamnatin tsakiya. Ko ma dai yaya batun yake wannan al’amari ne da zai taka muhimmiyar rawa dangane da sakamakon zabe, don haka ya zama tilas INEC ta dauki kwakkwaran mataki. Ba tun yau ake gudanar da zabe a kasar nan ba, bai kamata a samu matsala irin wannan ba, ya kamata a ce matsalar raba katin zabe ta zama tarihi. A ce rijistar wadanda za su kada kuri’a da samar da katunan zabe da kuma rabawa sun sanya a rika tayar da jijiyar wuya, wannan ba zai haifar wa kasar nan da mai ido ba, tilas INEC ta dauki matakin gaggawa. Batun cewa ‘hukumar ta rasa kundin sunayen wadanda suka yi rijista’ ba zai gamsar da jama’a ba.
An rawaito Gwamnan Jihar Legas Babutunde Fashola na tayar da jijiyar wuya dangane da wannan matsalar rabon katin zaben da aka fuskanta, ya ce wannan abin kunya ne ga INEC, sannan hankali ba zai dauka ba, a ce INEC ta fake da dalilin bacewar sunayen wadanda suka yi rijista da ita, wanda hakan ya sanya a Jihar Legas sunayen mutane fiye da miliyan 1 suka bace.
Mai magana da yawun Shugaban Hukumar INEC, Mista Kayode Idowu ya ce INEC ba ta goge sunayen wadanda suka yi zabe miliyan 1 da dubu 400 wadda ta tattara a Jihar Legas  ba, don haka wadanda suka gudanar da zabe a shekarar 2011 yawansu miliyan 6 da dubu 100 ne, amma a lokacin da aka sanya sunayen a wata manhaja da ke tantance mutane ta hanyar amfanin da tambarin yatsunsu, sai aka samu adadin mutane 82,892 wadanda suka yi rijista fiye da daya.
Fashola ya ce wannan ba hujja ce mai gamsarwa daga wurin INEC ba, ya kamata a fahimci abin da mutane suke gani ne, idan aka hana miliyoyin jama’a kada kuri’a a lokacin zabe mai zuwa hakan ba zai haifar da da mai ido dangane da sakamakon zabe ba.
An samu korafe-korafe dangane da rabon katin zabe na dindindin a jihohin Kano da Ribas da Katsina da Barno da Imo da sauransu, wannan babban kalubale ne ga INEC, ya kuma zama dole ta samar da ingantattun hanyoyin da katunan zabe za su kasance a hannun jama’a, wanda yin hakan zai dawowa da hukumar darajarta, ba kamar yanzu da jama’a ke dari-dari da ita ba. Bai kamata hukumar ta tsaya a kan cewa ba ta da wata boyayyiyar manufa dangane da rabon katin zabe na dindindin ba, ya zama dole ta fahimci  matsalar da ake ciki, sannan ta dauki matakin gaggawa don ba kowane dan Najeriya damar kada kuri’a ba tare da wata fargaba ba, ko da hakan ya kunshi kada kuri’a ta hanyar ’yar tike ne.