✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar IMF ta dakatar da bai wa Mozambikue bashin kudi

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF, ya dakatar da bai wa Mozambikue kudi bayan ya gano cewa gwamnatin kasar ta ki bayyana basukan da…

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF, ya dakatar da bai wa Mozambikue kudi bayan ya gano cewa gwamnatin kasar ta ki bayyana basukan da ake binta na sama da dala biliyan daya, kamar yadda BBC ta bayyana.
Wani wakilin IMF ya ce mai yiwuwa ma wasu kasashen su ma su bi sahu wajen dakatar da tallafin da suke bai wa kasar.
Wannan dai zai sa matsi a kan Mozambikue wadda ta dogara da tallafi daga kasashen waje domin tafiyar da kashi daya cikin hudu na kasafin kudinta.
Da ma kasar tana fuskantar matsalar tattalin arziki, domin haka ne ma haka Firaministan Mozambikue ya tafi Amurka domin kokarin neman sulhu da manyan kasashen da ke ba su tallafi.