✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Hisba ta gargadi masu badala a Jigawa

Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa ta gargadi masu sayar da giya da sauran kayan da ke jihar su kaurace wa haka saboda hukumar ta dauki…

Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa ta gargadi masu sayar da giya da sauran kayan da ke jihar su kaurace wa haka saboda hukumar ta dauki matakan kai samame a  lungu da sako na jihar da ake aikata badala da miyagun ayyuka.

Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa Malam Ibrahim Dahiru Garki ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira, inda ya ce abin da ya sa suka tsagaita kai samame gidajen da ake zargin aikta laifi shi ne saboda lokaci ne na siyasa, kada a mayar da harkar siyasa, amma tunda an kammala zabe za su dukufa ga yin aiki ba dare ba rana.

Ya bayyana nasarorin da suka samu a tsawon shekara hudu na millkin Gwamna Badaru Abubakar, inda ya ce daya daga ciki suna zuwa wuraren ibada a fadin jihar don ba da tsaro, kuma sun yi wa mutum 9,321 sulhu, sannan sun yi wa ’yan kasuwa 411 sulhu da yin sasanci a tsakanin iyayen yara 703 da kuma yin sulhu a tsakanin manoma da makiyaya  3,299.

Ya ce an yi wa makwabta 103 sulhu, wanda sulhun da suka yi ya kama mutum 13,837 a cikin shekara hudu na mulkin Gwamna Badaru. Ya ce yayin da jami’an Hisba suke yin sintiri a tsawon shekara 4, an samu nasarar rufe gidajan giya da na sharholiya guda 194 kuma sun baza dabar shaye-shaye 79 da cibiyoyin kade-kade  104 yayin da suka kori bokaye da ’yan damfara 616 daga jihar.

Ya  ce sun mayar da almajirai 117 gidajen iyayensu saboda samunsu da fadawa cikin wani hali na rayuwa sabanin na almajiranci kuma an mayar da mahaukata da wadanda aka yi wa auren dole hannun iyayensu mutum 514.

Ya ce su kuma mayar da karuwai 204 zuwa jihohinsu na asali a kokarin hukumar na hana karuwanci, sai kuma mayar da yara masu yawon banza 25 hannun iyayansu.