✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar DPR ta gargadi gidajen mai kan sayar da fetur ga masu jarka

Hukumar Kula da Harkokin Man fetur ta kasa (DPR) ta gargadi masu gidajen man fetur a Jihar Adamawa su daina sayar da man fetur a…

Hukumar Kula da Harkokin Man fetur ta kasa (DPR) ta gargadi masu gidajen man fetur a Jihar Adamawa su daina sayar da man fetur a boye ga masu saya a jarka ko ta karbe lisisinsu.

Shugaban Hukumar a Jihar Adamawa da Taraba, Mohammed Alaku ya bayyana wa manema labarai haka a lokacin da ya kai ziyarar ba-zata a gidajen mai a jihar.

 Ya tuhumi wasu gidajen man fetur cewa su ne ummul -haba’isin kawo karancin man fetur a jihar, domin mafi yawansu suna sayar da man fetur din fiye da Naira 145 kan kowace lita, kamar yadda gwamnati ta kayyade. 

Alaku ya dauki alkawarin bata wa kowane mai gidan man fetur idan ya kama shi a cikin wadanda ke neman bata wa wannan gwamnati suna, wajen sayar da man fetur fiye da kayyadadden farashi na Naira 145.

 Mohammed Alaku ya kai ziyarar ba-zata zuwa karamar Hukumar Fufore da ke kan iyaka da Kamaru, inda ya ce yana so ya tabbatar da cewa ana sayar da man fetur yadda gwamnati ta kayyade, domin rage masu sayen fetur a jarka.

 A cewarsa, ya umarci ma’aikatansa da su rika kai ziyarar ba-zata, domin ganin yadda kowane gidan man fetur ke sayar da man fetur da kuma irin farashinsa.

Alaku ya kirayi direbobi a Jihar Adamawa da Taraba da su kara hakuri game da matsalolin man fetur, kuma da yardar Allah sun kusa magance matsalar man fetur.