✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukuma ta wayar da kan jama’a kan Aikin Hajjin bana

Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Birnin Tarayya, Abuja ta fara gangamin wayar da kan jama’a a yankin game da abin da ya shafi…

Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Birnin Tarayya, Abuja ta fara gangamin wayar da kan jama’a a yankin game da abin da ya shafi tsare-tsare da dokokin gudanar da Aikin Hajji a bana.

A yayin gangamin, manyan jami’an hukumar sun ziyarci gidajen watsa labarai da sarakunan gargajiya, domin neman hadin kansu wajen tabbatar da inganci da nasarar Aikin Hajjin bana.

A ziyarar da suka kai wa Ona na Abaji, Alhaji Adamu Baba Yunusa, Daraktan Hukumar Malam Muhammad Bashir, ya nemi sarakunan su albarkaci tsare-tsaren hukumar tare da wayar da kan maniyyata a yankinsu, game da sababbin tsare-tsare da dokokin da hukumar ta shigo da su kan tafiyar da Aikin Hajji a bana.

Ya ce a bana, hukumomin Saudiyya da na Najeriya sun gabatar da wasu sababbin tsare-tsare, wadanda za su taimaka wa maniyyata wajen gudanar da Hajji Karbabbe.  Ya bayyana cewa hukumarsa a shirye take wajen kyautata wa maniyya a dukan wuraren da suka wajaba cikin inganci da karramawa tun daga gida Najeriya, har zuwa da dawowa daga kasa Mai tsarki.

A nasa bangaren, yayin da yake amsar bakuncin ayarin hukumar, Ona na Abaji kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Abuja, Alhaji Adamu Baba Yunusa, ya yi kira ga jami’an hukumar su jajirce wajen inganta aikinsu na kyautata jin dadin maniyyatan da za su sauke farali a bana. Ya nanata muhimmancin da ke tattare da Aikin Hajji a rayuwar Musulmin da suka samu zarafi. Don haka ya gargade su da su kiyaye aikata duk wani abu da zai bata sunan kasarsu.

A ci gaba da ziyarar, Daraktan ya gargadi al’ummar Fulanin yankin Abuja su guji yin mu’amala da ’yan kamasho wajen biyan kudin Hajji. Ya yi wannan gargadi ne a fadar Sarkin Jiwa, inda ya ce gargadin ya zama wajibi, ganin yadda maha’inta da ’yan damfara ke cutar Fulani a irin wannan lokaci, musamman ganin cewa wadansu daga cikinsu ba su da ilimin yadda ake biyan kudin kujerar Aikin Hajji. Ya gargade su kan su  kiyayi biyan kudi kai-tsaye ga wadansu da sunan kudin kujera, alhali ka’idar hukumar ita ce ana biya ne ta hanyar bankuna.

Da yake jawabi, Sarkin Jiwa, Alhaji Idris Musa ya nuna muhimmancin fadakarwa game da abin da ya shafi al’amuran Aikin Hajji. Ya ce a shirye fadarsa take wajen taimaka wa hukumar domin fadakar da jama’a kan hanyoyin biyan kudin Aikin Hajji da kuma yadda ake gudanar da shi.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Muhammad Lawal Aliyu, ya shaida wa Aminiya cewa a karshen wannan wata ne za a rufe karbar kudin ajiya daga maniyyata, don haka ya yi kira ga dukan maniyyata su hanzarta kammala biyan jimillar kudaden kujerunsu kafin karshen watan.