A kokarinta na kawo karshen hare-haren da ya addabi mutanen Zangang da ke kan iyakar kananan hukumomin Kaura da ke Jihar Kaduna da kuma na Ryom, da ke Jihar Filato, Hukumar Zaman Lafiya ta Jihar Kaduna ta shirya bita ga al’ummomin masarautar Attakar da ke karamar hukumar Kaura da na Ganawuri da ke Jihar Filato inda aka dade ana rikici a tsakaninsu.
Da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar a fadarsa da ke Karamar Hukumar Kaura, Sarkin Attakar (Agwam Takad), Mista Tobias Wada Nkom, ya bayyana dadadden rikicin da ke tsakanin kabilun Atakar da Fulani a daya gefen, da kuma tsakanin Atakar da Fulani da mutanen Atein da ke Ganawuri a matsayin babban abin takaici.
- An amince da kara wa Sakatarori 11 girma a Adamawa
- Batanci ga Annabi: An dage zaman kotu saboda rashin lauya
Ya ce sun fara dandana zaman lafiyar da ta fara samun gindin zama albarkacin tarurrukan zaman lafiya da kuma shiga tsakani da Hukumar Zaman Lafiya ke yi abin da ya sa babu wani abu da ya sake faruwa a yankin tun bayan harin watan Afrilun bana.
“Mun gayyato tare da tattaunawa da Eriya Kwamanda na ’yan sandan yanki na Kafanchan, da Kwamandan Sojoji da sauran shugabannin jami’an tsaro inda muka fahimci Atakar da Fulani ne kawai za su iya samar da zaman lafiya a tsakaninsu, amma ba jami’an tsaro ba.
“Mun kafa kwamiti a watan Agusta wacce ta kunshi kabilun Atakar da Fulani kuma mun ba Bafulatani jagorancinta wacce za ta duba yanayin yiwuwar daukwar kowa zuwa muhallinsa.”
Sarkin ya ce matsalar kan iyaka na daga cikin manyan dalilan tashe-tashen hankula a yankin, inda ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta shigo cikin lamarin don magance matsalar kan iyakan.
Sannan ya bukaci Atta na Atein da ke Jihar Filato da ya nada wa ’yan kabilar Attakar Hakimi a cikinsu lura da yawan ’yan kabilar da ke yankinsa a jihar ta Filato domin a cewarsa, hakan zai kara kulla zumunci da kuma samar da wata hanya ta samun bayanan sirri wanda za su taimaka wajen hadin kai da zaman lafiya.
Da take nata jawabin, Kwamishiniya a Hukumar Zaman Lafiya ta Jihar Kaduna, Hajiya Khadija Gambo Hawaja ta yi kira ne ga dukkanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna da su mayar da takubbansu cikin kube tare da girmama juna a matsayinsu na ’yan Adam.