Kocin kulob din Leicester City ya bayyana hudubar da ya yi wa ’yan kwallonsa a ranar farko da ya fara horar da su a Ingila ta yi matukar tasiri, ganin cewa har yanzu su ke saman tebur a gasar rukunin firimiya na Ingila ana saura wasanni hudu a kammala gasar.
dan asalin Italiya, kocin City Claudio Raneri ya ce hudubar da ya yi musu ita ce, da zarar an fara gasar firimiya ta Ingila su rika fuskantar kowane irin wasa ba tare da nuna tsoro ko shakkar wani kulob ba komai girmansa. Hasalima komai girman kulob kada su ji tsoron haduwa da shi, illa dai su mayar da hankali da nuna kwazo da hakan zai iya sanya wa su samu nasara.
Ya ce ya nuna wa ’yan kwallon cewa a wasa tilas ne abu uku su faru, ko dai a samu nasara, ko akasin haka ko kuma a yi kunnen doki, don haka idan aka doke Leicester City ba sabon abu ba ne tun da kulob ne da yake tasowa.
Ya ce ’yan kwallonsa irin su N’Golo Kante da Jamie bardy da Wes Morgan da Danny Drinkwater da Riyad Mahrez ba su yi fice a duniya ba don haka da yawa daga cikin magoya bayan kwallon kafa ba su dauki kulob din Leicester a matsayin wani kulob da zai tabuka abin kirki a gasar ba. “Ga shi a yanzu wadannan ’yan kwallo sun ba marada kunya inda wadansu manyan kulob a ciki da wajen Ingila suka fara zawarcinsu”, inji Raneiri.
Hudubar da na yi wa ’yan kwallona kafin a fara gasar firimiya ta bana ta yi tasiri – Kocin Leicester City
Kocin kulob din Leicester City ya bayyana hudubar da ya yi wa ’yan kwallonsa a ranar farko da ya fara horar da su a Ingila…