✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda aka yi bikin Ranar Takutaha a Kano

Jama'a ke hawa dutsunan Dala da Goron Dutse da sauran abubuwa na sada zumunci da ibabada da sauransu.

A ranar Laraba 4 ga watan Oktoba a ka yi bikin ranra Takutaha, wadda ake murna a matsayin ranar bakwai bayan Mauludin Manzon Allah (SAW).

Ga wasu hotunan yadda ranar ta kasance a Kano, inda jama’a ke hawa dutsunan Dala da Goron Dutse da sauran abubuwa na sada zumunci da ibabada da sauransu.

Hotuna: Abba Adamu.

Dandazon wasu mata a cikin garin Kano a lokacin bikin Takutaha a ranar Laraba 5 ga Oktoba, 2023. (Hoto: Abba Adamu).
Masu bikin takutaha a lokacin da suke hawa Dutsen Dala a ranar Takutaha a Kano. (Hoto: Abba Adamu).
Masu tattakin bege a ranar Takutaha ta shekarar 2023 a birnin Kano. (Hoto: Abba Adamu).
Yadda mutane suka yi dafafi suna tattaki a birnin Kano a ranar Takutaha a Kano, ranar Laraba 4 ga Oktoba, 2023. (Hoto: Abba Adamu).
Motar DJ da masu begen Manzon Allah (SAW) a yayin tattaki ranar Takutaha a Kano. (Abba Adamu).