Hotunan ganawar shugabannin Fulani da Gwamnatin Ogun
Tattaunawa kan rikicin Fulani makiyaya da manoma a Gidan Gwamnatin Ogun
DagaAbbas Dalibi
Tue, 16 Feb 2021 15:07:24 GMT+0100
Shugabanin Fulani makiyaya sun isa Jihar Ogun don ganawa da mahukuntan Jihar kan matsalar rikicin Fulani makiyaya da manoma a jihar.
Jihar Ogun ta yi fama da rikice-rikicen Fulani makiyaya da manoma a kwanakin nan, tun bayan da mai taratsin kare Yarbawa Sunday Adeyemi (Sunday Igboho) ya kai wa Fulani farmaki a yankin Eguwa da ke Karamar Hukumar Yewa ta Arewa a Jihar.
Shugabannin Fulanin sun kai ziyarar ce a karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar Miyyeti Allah (MACBAN), Alhaji Kirwa Hardon Zuru.
Wani sashe na tawagar shugabnnin al’ummar Arewa da suka halarci tattaunwar ta ranar Talata a Gidan Gwamnatin Jihar Ogun.Wasu daga cikin shugabannin Yarabawa da suka halarci zaman da aka yi a Gidan Gwamnatin Jihar Ogun.Tawagar shugabannin Kungiyar MACBAN sun ziyarci al’ummar Fulani makiyaya a Jihar.Wasu Fulani makiyaya da Shugannin kungiyar suka gana da su a yayin ziyarar.Wasu daga cikin mahalarta ganawar shugabannin Kungiyar Miyetti Allah da makiyaya.Wasu al’ummar Arewa a kusa da jami’an tsaro da aka girke domin tabbatar da doka da oda.Wani sashe na shugabannin al’ummar Yarabawa da suka halarci zaman da aka yi a Gidan Gwamnatin Jihar.Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan rikicin kabilanci da na tsakanin manoma da makiyaya a Jihar.