✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hotunan bikin ba wa Sarkin Katagum na 12 Sanda

Manya-manyan sarakunan Arewa ne suka halarta tare da manyan jami'an gwamnati da kuma dandazona jama'a daga ciki da wajen jihar Bauchi.

A ranar Asabar ne aka yi bikin ba wa Dokta Faruk na II sanda a matsayin Sarkin Katagum na 12 a Azare.

Manya-manyan sarakunan Arewa ne suka halarta tare da manyan jami’an gwamnati da kuma dandazona jama’a daga ciki da wajen jihar Bauchi.

Ga wasu kayatattun hotunan bikin:

Isowar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ada Abubakar wurin taron bikin (Hoto: Sani Maikatanga)
Isowar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, wurin taron. (Hoto Sani Maikatanga)
Isowar Sarkin Katagum dandamalin manyan baki inda za a ba shi sandar (Hoto Sani Maikatanga).

Ana mika wa Sarkin Katagum takobin masarautar (Hoto Sani Maikatanga)
Mika wa Sarkin Katagum Al-Kur’ani Mai Girma na masarautar. (Hoto Sani Maikatanga).
Ana rantsar da sarkin domin kama aiki (Hoto Sani Maikatanga).
Gwamnan Jihar Bauchi, Snata Bala Mohammed yana sa hannu a kan takardar nadin sarautar Sarkin na Katagum. (Hoto Sani Maikatanga)
Sarkin na karbar gaisuwa daga Gwamnan Bauchi bayan ya ba shi sanda .(Hoto Sani Maikatanga).
Ministan Ilimi Adamu Adamu a wajen bikin. (Hoto: Sani Maikatanga)
Sarkin Gumel Ahmed Mohammed Sani da daya daga cikin sarakuna a wajen taron bikin. (Hoto Sani Maikatanga)
Sarkin Ringim, Sayyadi Mahmoud Ringim a wajen taron bikin. (Hoto Sani Maikatanga).
Wasu daga cikan manyan bakin da suka halarci taron bikin.
Shugaban Darikar Kadiriyya, Shiekh Karibullah Nasiru Kabara, da dan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a wajen taron bikin. (Hoto: Kamal Photos)
Dandazon jama’ar da ta taru a filin taron. (Hoto Sani Maikatanga)
(Hoto Sani Maikatanga)