Kimanin wata daya ke nan da girgizar mafi muni a kasar Turkiyya ta ci rayuka 50,000 da kuma raba miliyoyin mutane daga muhallansu.
Wadannan wasu ne daga cikin hotunan abubuwan da suka faru sanadiyyar girgizar kasar Syria da Turkiyya a ranar 6 ga watan Fabrairu.
Wani uba ke nan rike da hannun ‘yarsa da ta rasu a karkashin buraguzan ginin da ya danne ta sanadiyyar girgizar kasa.Wannan kuma wata jinjira ce da aka ceto a buraguzon gini bayan mahaifiyarta ta haife ta bayan girgizar kasar.A nan kuma ma’aikatan ceto ne ke kokarin fito da gawar wata budurwa ‘yar shekara 17 a karkashin buraguzan ginin da ya danne ta.Yadda wasu jami’an agaji ke kokarin ceto mutanen da suka makale a karkashin gini.Wani katafaren gini da girgizar kasar ta rusa a Turkiyya
Yadda aka ceto wata karamar yarinya a karkashin buraguzan ginin da ya rushe.