Mai martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi, ya gudanar da bikin Hawan Daba a Kofar Fadar Shehun na Borno da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Wannan hawan dai a bana ya sa mu halartar manya-manyan baki daga Masarautar ta Borno, ciki har da kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno- Abdulkarim Lawan, tsohon Gwamnan Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, tsohon Mataimakin Gwamna, Alhaji Usman Mamman Durkwa da manyan jami’an gwamnati da shugabannin siyasa da dama ne suka halarci Sallar Idi a daidai lokacin da dubban masallata suka yi sallah.
Bayan sallar idi, mazauna birnin Maiduguri sai kuma su ka ci gaba da nuna murnar su ta wajen gudanar da hawan na Dabar wajen hawan dawakai da nuna kwarewa daga mahayansu don burge manyan baki da kuma al’ummomin da suka halarci dandalin a Kofar Fadar Shehun.
Bikin hawan Durbar dai, wani biki ne na al’adu da ake yi da dawaki ake gudanarwa a kowace shekara a garuruwan arewacin Najeriya da suka hada da Borno, Kano, Katsina, Sakkwato, Zazzau, Bauchi, Bida, Ilorin da sauran su.
An sami nunin raye-rayen al’adu daban-daban yayin da masu rawa ke motsawa cikin aiki tare da ganguna da kidan da ake yi da ganguna da bushe-bushmen algaita a wajen wannan bikin hawan.
Ga wasu daga cikin hotunan hawan: