✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda Sanusi II ya yi hawan sallah a Kano

Sarkin ya yi hawan ne duk da umarnin 'yan sandan jihar na haramta hawa a sallar bana.

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya gudanar da hawan Sallah, bayan jagorantar Sallar Idi a Masallacin Juma’a da ke Kofar Mata da ke jihar.

Ya jagoranci Sallar Idin ne, a Masallacin Juma’ar, sakamakon mamakon ruwan sama da aka tashi da shi, wanda ruwan ya hana sallah a filin Idi.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusif, da sauran manyan jami’an gwamnatin jihar sun yi Sallar idin ne tare da Sarki Sanusi.

Wannan dai na zuwa ne bayan da rundunar ’yan sandan jihar ta haramta hawan Sallah a Jihar sakamakon dambaruwar masarautar Kano.

Matakin da tuni gwamnatin jihar, ta ce hurumin gwamnan jihar ne, ya ayyana ko za a yi hawan sallah ko ba za a yi ba, kasancewarsa lamba ɗaya a ɓangaren kula da harkokin tsaron jihar.

Ga hotunan yadda hawan ya kasance a jihar: