Matafiya da suka yi dafifi domin zuwa garuruwansu kyauta a jirgin ƙasa, suka yi cirko-cirko a safiyar Talata a Tashar Jirgin Ƙasa ta Idu da ke Abuja.
Sai da lokacin hawa jirgin ya yi jami’an tashar suka sanar da jama’a cewa an ɗage lokacin da awa huɗu, zuwa ƙarfe biyu na rana.
Gwamnatin Tarayya ta ɗauki nauyin tafiye-tafiye a jirgin ƙasan kyauta a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.