Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce an garzaya asibiti da mutanen da suka yi rauni sakamakon harin da aka kai a hanyar da wani jirgin kasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna yake wucewa a daren Litinin.
Wata sanarwa mai dauke da sa-hannun Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ta ce tuni jami’an tsaro suka kai wadanda abin ya shafa don a ba su kulawa ta gaggawa.
- Jirgin Kasa Makare Da Fasinjoji Daga Abuja Zuwa Kaduna Ya Taka ‘Bam’
- Mahaifin Almajirin Da Aka Yi Wa Kaca-Kaca Da Duka Ya Ce Bai San Dansa Na Kano Ba
“Ana kokarin kwashe fasinjojin [jirgin] daga wurin [da lamarin ya faru], kuma an garzaya da wadanda suka jikkata asibiti don a ba su kulawa ta gaggawa”, inji Mista Aruwan.
Sai dai sanarwar ba ta fadi adadin mutanen da suka jikkata ko yawan mutanen da suke cikin jirgin ba.
“Gwamnatin Jihar Kaduna za ta yi aiki kafada da kafada da Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) don samun cikakken jerin sunayen fasinjojin jirgin don a tantance su”, inji Kwamishinan.
Fasinjojin jirgin kasa
A daren Litinin ne dai jirgin, wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna makare da fasinjoji, ya yi tuntube da wani abu mai fashewa da ake zargin bam ne a tsakanin Katari da Rijana a Jihar ta Kaduna.
Jirgin, wanda ya tashi da karfe 6 na yamma daga tashar Idu a Abuja, ya taka “bam” din ne dai minti kusan 30 kafin ya isa tashar jiragen kasa ta Rigasa.
A sanarwar tasa dai, Mista Aruwan ya bayyana yadda ya ce Gwamnatin Kaduna ta samu rahotanni da dama game da harin, kuma ba tare da bata lokaci ba ta sanar da hukumomin da abin ya shafa, su kuma nan take suka tura jami’ansu don kai dauki.
Ya kuma ce Gwamna Nasir El-Rufai na tuntubar jami’an tsaro, wadanda suke ci gaba da binciken yankin don ceto wadanda abin ya rutsa da su, a-kai-a-kai.
Babu cikakken bayani
Har yanzu dai babu cikakken bayani game da faruwar lamarin.
“Babu cikakken sabis din waya a wajen da lamarin ya faru ballantana mu san me ya faru a can, dole sai jami’an da muka tura sun dawo kafin mu san hakikanin abin da ya faru,” inji wata majiya ta jami’an tsaro a Kaduna.
“Abin da muka sani shi ne an dasa bam a kan titin jirgin, kuma jirgin ya sauka daga kan layinsa,” inji majiyar.
Sai dai wasu majiyoyin sun ce maharan sun rika harbi kan mai uwa da wabi, a kokarinsu na kwashe fasinjojin.
Wani hoton bidiyo da aka wallafa a kafafen sadarwa na zamani, wanda Aminiya ba ta iya tantance sahihancinsa ba, ya nuna wani mutum da rauni a hannu wanda aka tambaya ko harsashi ya same shi, ya ce e.
Ana kiyasta cewa jirgin ya dauko fasinjoji sama da 700 a lokacin da lamarin ya faru.
Ba wannan ne karo na farko ba da aka dasa ababe masu fashewa a kan titin jirgin na Abuja zuwa Kaduna.
Wasu dai na ganin wannan wata dabara ce ta ‘yan bindiga ta jefa tsoro a zukatan masu hawa jirgi don su bi hanyar mota washegari a tare su.