✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

HOTUNA: Yadda INEC ta bai wa Abba shaidar lashe zaben Gwamnan Kano

Abba Kabir Yusuf ya kayar da Nasiru Yusuf Gawuna a zaben gwamnan Jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta bai wa Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP takardar shaidar lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Abba ya kayar da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC, wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar.

Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta ki amincewa da sakamakon zaben, inda ta bukaci INEC da ta sake duba shi.

Hakan ya sanya jam’iyyar shiga zanga-zanga a makon da ya gabata, amma INEC ta ce su garzaya kotu don neman hakkin da suke ikirari.

Ga wasu daga cikin hotunan yadda bikin bayar da shaidar lashe zaben ya gudana: