Dubban al’ummar Musulmi a Jihar Kano, sun gudanar da bikin Takuhata, wanda aka saba yi a ranar 19 ga watan Rabi’ul Auwal (sati ɗaya daga 12 ga Watan Rabi’ul Auwal), don murnar ranar sunan Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW).
Wasu daga cikin waɗanda suka yi bikin sun sanya fararen kaya, wasu kuma suka sanya wasu launukan kaya na daban.
- Zaɓen Gwamna: APC ta kama hanyar lashe zaɓen Edo
- Mazauna gaɓar Kogin Benuwe sun soma ƙaurace wa gidajensu
Mutane sun yi wa manyan titunan jihar ƙawanya, inda suka dinga rera waƙoƙin yabon Annabi.
Aminiya ta ruwaito yadda aka gudanar da bikin Maulidin bana a faɗin ƙasar nan.
Ga hotunan yadda bikin Takutaha ya gudana a Kano: