✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi bikin daukar gawar Fir’aunoni a Masar

Dubun-dubatar mutane sun yi dafifi a kasaitaccen bikin da aka kashe wa miliyoyin Daloli

An gudanar da wani gagarumin shagalin bikin canza wa Fir’aunoni 22 kaburbura daga Birnin Alkahira Kasar Masar zuwa sabon gidan tarihin kasar.

Dubun-dubatar mutane sun yi dafifi a ranar Asabar da dare domin ba wa idanunsu abinci a kasaitaccen bikin da aka kashe wa miliyoyin Daloli domin daukar Fir’aunonin 22 —maza 18 mata hudu— a wata tafiya mai tsawon kilomita bakawai daga Dandalin Tahrir zuwa sabon gidan adana tarihi a Fustat.

Hukumomin kasar sun rufe manyan hanyoyin yankin Kogin Nilu domin nuna girmamawa Fir’aunonin, wadanda mahayan dawakai 150 da babura 60 suka yi wa rakiya a kasar  mai tunkaho sarakunan da suka rayu shekaru 1600 kafin Annabi Isa (AS).

An dauki gawarwakin a motocin alfarma da aka tanada domin bikin. Kowane Fir’auna da motar da aka ware wa gawarsa dauke da sunansa. Hoto: AFP.
An yi amfani da kekunan dawakin zamanin Fir’aunoni a bikin domin tuno da rayuwar  shekaru aru-aru da suka wuce. Hoto: Aljazeera
Mutane sun yi dafifi domin girmamawa ga Fir’aunonin lokacin da ake wucewa da gawarwakinsu  a birnin Alkahira. Hoto: AFP.
An yi kade-kade da raye-raye na shekaru aru-aru a lokacin bikin da babu masaka tsinke a birnin Alkahira.
Masu nishadantar da jama’a sanye da kayan tarihin kasar Masar lokacin da suka nishadantar da masu kallo yayin bikin. Hoto: AFP
Jerin gwanon motocin da suka dauko gawarwakin Fir’aunonin a kusa da sabon gidan tarihin. Hoto: AFP.
Motocin a shataletalen da aka yi na musamman domin sabon gidan tarihin. Hoto: AFP.
An yi fareti na musamman inda mahaya 210 suka yi wa Fira’uonin rakiya zuwa sabon makwancinsu.
Badujala suna kayatar da masu kallo a lokacin bikin a gaban gidan tarihin da ke Fustat. Hoto: AFP.
Sabon gidan tarihin da aka kaddamar inda a nan aka yi wa Fir’aunonin sabon matsuguni. Hoto: AFP.