An gudanar da wani gagarumin shagalin bikin canza wa Fir’aunoni 22 kaburbura daga Birnin Alkahira Kasar Masar zuwa sabon gidan tarihin kasar.
Dubun-dubatar mutane sun yi dafifi a ranar Asabar da dare domin ba wa idanunsu abinci a kasaitaccen bikin da aka kashe wa miliyoyin Daloli domin daukar Fir’aunonin 22 —maza 18 mata hudu— a wata tafiya mai tsawon kilomita bakawai daga Dandalin Tahrir zuwa sabon gidan adana tarihi a Fustat.
- ’Yan sanda sun kwato mutum 15 daga ’yan bindiga a Kaduna
- COVID-19: Mutum 7 sun mutu bayan karbar rigakafin AstraZeneca a Birtaniya
Hukumomin kasar sun rufe manyan hanyoyin yankin Kogin Nilu domin nuna girmamawa Fir’aunonin, wadanda mahayan dawakai 150 da babura 60 suka yi wa rakiya a kasar mai tunkaho sarakunan da suka rayu shekaru 1600 kafin Annabi Isa (AS).