✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda ake ci gaba da shari’ar Kwankwaso kan kudin ’yan fansho

An shirye-shiryen soma sauraron shari'ar a Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako da ke Kano kan wannan shari'a.

A Litinin din nan za a ci gaba da shari’ar tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, kan zargin karkatar da kudaden ’yan fanshon jihar.

A halin yanzu an shirye-shiryen soma sauraron shari’ar a Babbar Kotun Tarayya da ke zamanata a Sakatariyar Audu Bako da ke Kano kan wannan shari’a.

Tuni lauyoyin bangarorin da ke shari’ar suka riga suka zauna.

Hukumar Yaki da Masu Yi wa tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) ce ta gurfanar da jagoran na Jam’iyyar NNPP.

Kwankwaso ya kasance Gwamnati Kan daga 1999-2003 da kuma 2011 zuwa 2015.