A ranar Talata Allah Ya yi wa Sarkin rasuwa a Abuja, sakamakon rashin lafiya, yyana da shekara 79.
DagaSagir Kano Saleh
Wed, 1 Feb 2023 19:19:16 GMT+0100
Dubban mutane daga wurare daban-daban ne suka halarci jana’izar Sarkin Dutse, Marigayi Alhaji Nuhu Muhammad-Sanusi, wadda aka gudanar a ranar Laraba.
A ranar Talata Allah Ya yi wa Sarkin rasuwa a Abuja, sakamakon rashin lafiya, yyana da shekara 79.
Ga wasu daga cikin hotunan jana’izar da aka gudanar.
Dandazon mutane, babu masaka tsinke a lokacin da aka gudanar da ta’aziyyar a ranar Laraba.Manema labarai da sauran mahalarta jana’izar sun yi ta kokarin daukar hotunan jana’izar, duk da cikar kwarin da wurin ya yi.Babu masaka tsinke a wurin da mutane daga sassa daban-daban suka zo domin halartar jana’izar sarkin da aka gudanara a Masarautar Dutse, Jihar Jigawa.Sarakuna da manyan mutane, attajirai da jami’an gwamnati sun yi fitar dango zuwa halartar jana’izar Sarkin Dutse.Mutane ne iya ganin mai kallo a filin da aka gudanar Sallar Jana’izar sarkin a ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu, 2023.