Matashin ya rasu yayin da yake barci da sanyin safiyar ranar Asabar a Abuja.
DagaAbubakar Muhammad
Sun, 5 Mar 2023 15:54:36 GMT+0100
Abdullahi, daya ne daga cikin ‘ya’yan tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha, ya rasu ne a lokacin da yake barci da sanyin safiyar ranar Asabar, kamar yadda ‘yar uwarsa Gamsu Sani Abacha ta bayyana.
An yi jana’izar marigayin a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja a ranar Lahadi.
Sabon zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya halarci jana’izar.Mahaifiyar marigayin, Maryam Abacha na karbar gaisuwaKashim Shettima da Gwamman Yobe, Mai Mala Buni a wajen jana’izar
Yadda aka yi jana’izar Abdullahi, da ga tsohon shugaban kasar mulkin soji, Janar Sani Abacha