✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hotuna: Mijin Zahra Buhari ya mallaki Zaki domin kiwon gida

Ahmed Muhammad Indimi, wands suruki ne ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya mallaki Zaki a matsayin dabbar kiwo. Ahmed wanda ya auri diyar shugaban kasar,…

Ahmed Muhammad Indimi, wands suruki ne ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya mallaki Zaki a matsayin dabbar kiwo.

Ahmed wanda ya auri diyar shugaban kasar, Zahra Buhari, ya wallafa wasu hotunansa tare da Zakin mai farin launi da zai zame masa abun debe kewa da shakatawa.

A sakon da Indimi ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya ce, “Sabon abun soyuwa a gare ni”, sannan a wani hoton kuma ya wallafa cewa, yana kaunar sabuwar dabbar kiwon da ya mallaka.

Ga wasu daga cikin hotunan da Indimi ya wallafa yana murmushi rike da sabon Zakin.

Ahmed Indimi rike da farin Zakinsa
Ahmed Indimi cikin murmushi rike da farin Zakinsa

A shekarar 2016 ne Ahmed Indimi, dan hamshakin attajirin nan, Muhammed Indimi, ya auri diyar shugaban kasar.

%d bloggers like this: