Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan Kafofin Sada Zumunta, Bashir Ahmad, ya shiga jerin masu neman taraka a zaben 2023.
Bashir Ahmad, yana zawarcin kujerar dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu na Jihar Kano a zaben da ke kara matsowa.
- Abin da Kwankwaso ya ce a wurin sayen fom din takarar shugaban kasar 2023
- Hotunan matsahin hafsan sojin da ya rasu a hatsarin jirgin Kaduna
Tuni fastocinsa suka fara yawo kuma ya riga ya gana da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kan neman takarar tasa.
A yayin da yake ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki a yankin mazabar, ga wasu daga hotunan: