HOTUNA: Bikin karrama Jakadiyar Birtaniya a Najeriya
An shirya kasaitacciyar liyafar cin abincin dare a gidan gwamnatin jihar domin karrama Jakadiya Catrina Liang
DagaYakubu Liman
Thu, 29 Sep 2022 7:45:05 GMT+0100
Jakadiyar Biritaniya a Najeriya, Catrina Liang, ta kai ziyarar kwanaki biyu Kebbi, a bisa gayyatar gwamnatin jihar.
A yayin ziyarar an shirya mata tarba ta musamman a wata kasaitacciyar liyafar cin abincin dare a gidan gwamnatin jihar domin karrama ta, in ji Yahaya Sarki, kakkin gwamnan jihar.
A taron an yi jawabai da raye-raye da wake-waken al’adun gargajiyar jama’ar jihar domin karrama bakuwar, sannan aka bai wa ayarinta kyautuka na alfarmarma.
Ga yadda taron ya kasance cikin a hotuna:
Isowar Jakadiya Catriana Liang tare da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi wurin taron liyafar (Hoto: Kakakin Gwamnan Jihar Kebbi).Jakadiya Liang da Gwamna Baguru tare da manya jami’an Jihar Kebbi a teburin cin abinci a yayin taron. (Hoto: Kakakin Gwamnan Jihar Kebbi).Wasu daga cikin ‘yan rakiyar jakadiya Liang a wurin liyafar (Hoto: Kakakin Gwamnan Jihar Kebbi).Gwamnan Bagudu tare da bakuwarsa a lokacin da ake taken kasashen Najeriya da Birtaniya. (Hoto: Kakakin Gwamnan Jihar Kebbi).Wasu daga cikin ‘yan rawar gargajiyar jihar suna cashewa a lokacin taron karramawar (Hoto: Kakakin Gwamnan Jihar Kebbi).Wasu daga cikin ‘yan rawar gargajiyar jihar a yayin taron. (Hoto: Kakakin Gwamnan Jihar Kebbi).Gwamna Bagudu da manyan jami’an gwamnatin jihar na mika kyauta ga daya daga cikin ‘yan rakiyar Jakadiya Liang. (Hoto: Kakakin Gwamnan Jihar Kebbi).Gwamn Bagudu da manyan jami’an gwamnatin jihar na mika kyautar alfarma ga jakadiyar (Hoto: SSA Media Governor Kebbi State)Gwamna Bagudu da manyan jami’an gwamnatin jihar tare da Jakadiya Liang da ‘yan rakiyarta bayan kammmala taron. (Hoto: Kakakin Gwamnan Jihar Kebbi).