✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hotuna: Asari Dokubo ya ziyarci Ganduje a Abuja

Asari ya ziyarci Ganduje don taya murnar zama shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Tsogon Jagoran Tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo, ya kai ziyarar taya murna ga shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje a Abuja.

Dokubo ya taya Ganduje murnar zama shugaban jam’iyya mai mulki ta kasa.

A wani sako da ta wallafa a shafin X (Twitter), jam’iyyar mai mulki ta ce tsohon gwamnan Kano, ya karbi bakuncin dan gwagwarmayar a gidansa da ke babban birnin tarayya, Abuja.

“Shugaba Abdullahi Umar Ganduje, ya karbi bakuncin Tsohon Jagoran Masu Tayar da Kayar Baya a Neja Delta, Asari Dokubo, a wata ziyarar taya murna a gidansa da ke Abuja,” in ji jam’iyyar.

Ga hotunan ziyarar a kasa: