✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hoton mutumin da yake daga hoton Tinubu a Ka’aba ya fara jawo cece-kuce

Mutane dai na ta Allah wadai da mutumin

Bayyanar hoton wani mutum da ya je aikin Umara a kasar Saudiyya aka gan shi yana daga hoton mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a masallacin Ka’aba.

Lamarin dai ya jawo Allah-wadai da cece-kuce musamman a kafafen sada zumunta na zamani.

Galibi dai mutane na ganin rashin dacewar hakan, musamman kasancewar shi wurin ibada mafi tsarki ga Musulmai.

“Allah ya isanmu da wannan mutumin, ya ci mutuncin addininmu,” inji wani mai suna Abubakar Hassan a shafinsa na Instagram.

Shi kuwa wani mai suna Bello Shehu ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “Muna kira ga hukumomin kasar Saudiyya da su dauki mataki tare da hukunta wannan mutumin.”

“Wannan wani nau’i ne na shirka fa. Ta yaya za ka daga hoton wani mahaluki a dakin Allah,” inji Aminu Sani.