Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce Hodar Iblis da miyagun kwayoyi sun mamaye Jihar Bauchi.
Kwamandan hukumar a Jihar, Segun Oke ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Bauchi yayin kaddamar da wani gangami kan yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi a Jihar.
Kwamandan ya kuma bayyana wurare da dama da ya ce ana amfani da su wajen hada-hadar kwayoyin a fadin Jihar.
“Muna ci gaba da binciken yadda ake shigo da Hodar Iblis zuwa Bauchi,” inji shi.
Kwamandan na NDLEA ya kuma ce sun kama mutane da dama da miyagun kwayoyi a fadin Jihar sakamakon samamen da suka gudanar.
A nasa jawabin yayin gangamin, Gwamnan Jihar, Bala Mohammed ya bayyana ta’ammali da miyagun kwayoyi a matsayin babban ummu-aba’isun kalubalen tsaro da sauran laifuka a kasa.
“Duk wanda ya ke ta’ammali da miyagun kwayoyi, abu na gaba da zai iya aikata wa shine laifi, dalilin kenan da ya sa muke fama da matsalar rashin tsaro,” inji Gwamna Bala.
Gwamnan, wanda ya sami wakilcin Babban Mai Ba shi Shawara Kan Harkokin Tsaro Janar Marcus Yake (mai ritaya) ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na taimakawa hukumar domin ta yaki harkar kwayoyin a Jihar.