✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hizbullah ta kai wa sojojin Isra’ila harin bom

Ƙungiyar Hizbullah ta ce mayaƙanta sun kai wa sojojin Isra'ila harin bom a wani kauye da ke Kudancin kasar Lebanon a safiyar Litinin.

Ƙungiyar Hizbullah ta ce mayaƙanta sun kai wa sojojin Isra’ila harin bom a wani kauye da ke Kudancin kasar Lebanon a safiyar Litinin.

Hakan na zuwa ne bayan Isra’ila ta sanar da tura ƙarin rundunar sojojinta domin aiwatar da yaƙinta da Hizbullah a Lebanon.

Ƙungiyar, wadda ta lashi takobin ci ba da yakar Isra’ila, ta ƙara da cewa, mayaƙanta “sun yi wa taron sojojin Isra’ila luguden bama-bamai a dandalin Maroun al-Ras.”

Ta fitar da wannan sanarwar ce bayan da farko ta ce mayaƙanta sun kai wasu hare-hare na daban kan sojojin Isra’ila a kan iyakar ƙasar Lebanon.

 

AFP.