Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta ce za ta samar wa hukumar Hisbah kotunan tafi-da-gidanka domin taimaka wa hukumar wajen gudanar da ayyukan shari’a a cikin sauki kuma a lokaci kankani.
Kwamishinan Shari’a, Barista Ibrahim Muktar shi ne ya bayyana hakan ga Babban Kwamadan Hukumar Hisbah a lokacin da ya kai ziyarar aiki a Ma’aikatar Shari’a da ke a Sakatariyar Audu Bako
da ke Kano.
Barista Ibrahim Muktar ya yi alkawarin ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin ingata ayyukan hukumar Hisbah tare da samar da kotun tafi-da-gidanka, domin magance yaduwar ayyukan badala da dangoginsu a Jihar Kano.
Kwamishinan ya yi jinjina ga hukumar Hisbah kan yadda dakarunta da jami’anta ke gudanar da aiki, musanman dakile badala da shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa da kuma hana karuwanci.
Ya kara da cewar samar wa Hisbah kotun tafi-da-gidanka, zai kara sanya tsoro a zukatan masu laifi.
Tun da fari da yake gabatar da jawabi, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dokta Harun Muhammad Sani Ibn Sina ya nuna bukatar hukumar, ta bangaren zamanantar da shari’u, samar da kudin shiga, da sauransu.
Dokta Harun Muhammad Sani Ibn Sina ya ce samar da kotun tafi-da-gidanka, baya ga saukaka yin shari’a, zai taimaka matuka wajen karya zukatan masu aikata laifi, irin na badala da na masu tsaikon biyan kudin shayarwa bayan aure ya mutu da masu yawon banza msanman ga ‘yan mata masu barin jihohinsu suna zuwa jihar.
Da yake nasa jawabin yayin ziyarar, Babban Daraktan Hukumar Hisbah, Dokta Aliyu Musa Aliyu Kibiya ya yi bayani mai tsawo a kan yadda hukumar ke fama da tarin matsaloli musamman karancin kudaden gudanar da aiyukan yau da kullum kamar su abin sufuri, da man fetur da sauransu da ciyar da masu laifi wadanda ake rike da su a hukumar.
Ya sake mika wata bukatan ga kwamishinan Shari’an ta a gyara wasu daga cikin dokokin Hukumar Hisbah domin su dace da zamani, kasancewar dokokin an samar da su ne tsawon lokaci.