Samari da ’yan mata 53 sun shiga hannun dakarun Hukumar Hisbah ta Jihar Kano saboda zargin aikata alfasha a birnin Kano.
Jami’an Hisbah sun yi ram da matasan ne suna suna tsaka da sayar da miyagun kwayoyi da kayan maye a layin a Lamido Crescent da ke Karamar Hukumar Nassarawa a daren Laraba.
- Turawa sun fi Larabawa taimaka wa Jihar Borno —Zulum
- Kotun Musulunci ta sa a kamo mawaki Rarara kan ‘boye’ matar aure
- Miji ya tsere bayan Matarsa ta haifi ’Yan hudu
- Me ya sa El-Rufai bai yi ta’aziyyar Iyan Zazzau ba?
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Lawal Ibrahim, ya ce wadanda aka kama din shekarunsu ba su hauwa 17 zuwa 19 ba, da suka hada da maza 27 da mata 26.
Sanarwar da ya fitar Laraba ta ce bayan samun bayanan sirri, dakarun Hisbah suka kai wa samarin da ’yan matan samame da misalin karfe 10 na dare, inda suka kama yayin da suke cikin sayar da kayan mayen.
Ya kara da cewa bayan tantance matasan, Hukumar ta gano cewa karon farko ke nan da aka taba kama matasan suna aikata laifi, don haka ta yi musu nasiha tare da mika su ga iyayensu.
Ya ce Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Haruna Ibn-Sina, ya gargadi matasa a Jihar da su guji aikata miyagun, su zama ’yan kasa na gari.