Askarawan Hisbah sun cafke wasu ’yan kasashen waje su biyu kan zargin su da aikata laifukan badala a Jihar Kano.
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Mujahid Aminuddeen Abubakar, ya ce ’yan ƙasashen wajen na daga cikin matasa 18 da jami’an hukumar suka kama kan aikata badala a sassan garin Kano.
Dokta Mujahid Aminuddeen Abubakar, ya ce, ’yan kasar wajen sun shiga hannu ne a wurin sharholiya bikin zagayowar ranar haihuwa.
“Mene ne na yin sharholiyar ranar haihuwa a wannan yanayi da jama’a suke fama da yunwa.
“Babban abin takaicin shi ne yadda aka hakura maza da mata, wanda hakan ya saba wa koyarwar Musulunci,” in ji shi.
A wani makamancin haka kuma, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta mika wa hukumar Hisbah wasu mata masu zaman kansu guda 38 da aka kama a Kwanar Gafan.
Daga cikin mata masu zaman kan nasu, har da masu tsohon ciki da masu kananan yara.
Hukumar Hisbah ta bayyana cewa akasarin matan masa zaman kansu sun fito ne daga jihohin Kaduna, Katsina, Kebbi da kuma Sakkwato.
Ta ce za tantance su da lafiyarsu sannan a dauki mataki na gaba.